6 Oktoba 2025 - 09:19
Source: ABNA24
Sudan: Ambaliyar Ruwa Ta Khartoum Ta Raba Sama Da Iyalai 1,200 Da Muhallansu

Ambaliyar ruwa a birnin Khartoum ta raba sama da iyalai 1,200 da muhallansu, a daidai lokacin da ake fama da matsalar rashin kayan tallafi na jin kai da kuma munanan illolin yakin da ake fama da shi a Sudan, a cewar wani rahoto da kungiyar kula da ‘yan cirani ta duniya ta fitar.

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na na Ahlul Baiti (AS) – ABNA– ya habarto cewa:  Hukumar Kula da Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (IOM) ta sanar da cewa, ambaliyar ruwa da ta afku a birnin Bahri na jihar Khartoum, ta raba sama da iyalai 1,200 da muhallansu, a daya daga cikin tashin hankalin da ya barke tun farkon damina. Kungiyar ta bayyana cewa gidaje biyar ne suka lalace gaba daya, yayin da akasarin sauran suka samu barna, lamarin da ya sa mazauna yankin da dama suka fice daga yankin. An lura cewa iyalai da abin ya shafa sun sami matsuguni na wucin gadi tare da al'ummomin da ke makwabtaka da su, wanda idan ba’a samar da mafita ta dindindin ko kuma matakan gaggawa ba wanna yanayi na iya hauhawa. Wannan bala'i na zuwa ne a daidai lokacin da Sudan ke fama da tashe-tashen hankula na tsaro, lamarin da ke kara dagula ayyukan jin kai da kuma kara takurawa ga ababen more rayuwa.

Dalilan Ambaliyar

Ambaliyar da aka yi a baya-bayan nan dai ta zo ne saboda karuwar ruwan kogin Nilu da magudanan ruwa da suka hada da kogin White Nile wanda ya samo asali daga tafkin Victoria da kuma Blue Nile da ke kwarara daga tsaunukan Habasha. Wadannan abubuwa na dabi’a, hade da ruwan sama kamar da bakin kwarya a lokacin watan Yuni zuwa Oktoba, sun taimaka wajen nutsar da manyan yankunan jihar Khartoum. Bisa kididdigar da aka yi a hukumance, sama da mutane 125,000 ne ruwan sama da ambaliyar ruwa ya shafa tun daga ranar 30 ga watan Yuni, lamarin da ke nuni da girman kalubalen da hukumomin yankin da kungiyoyin agaji ke fuskanta wajen shawo kan matsalar. Ambaliyar ruwa a Sudan wani lamari ne da ke ci gaba da faruwa, sai dai a bana an ga wani mummunan tashin hankali da ba a taba ganin irinsa ba, wanda ya zo daidai da rikicin soji da ke ci gaba da gwabzawa tsakanin sojoji da dakarun gaggawa.

Yanayin Yaki

Wannan bala'i na muhalli ya zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da yakin da ya barke a kasar Sudan a cikin watan Afrilun 2023 tsakanin sojojin kasar karkashin jagorancin Laftanar Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma Rundunar Taimakon gaggawa, karkashin jagorancin Mohamed Hamdan Dagalo (Hemedti). Rikicin ya bazu zuwa akasarin sassan kasar da suka hada da Khartoum, Darfur, Kordofan, Al-Jazeera, da Blue Nile, wanda ya yi sanadin mutuwar dubun-dubatar jama'a da kuma hijirar miliyoyin mutane a ciki da wajen kasar. Bisa kididdigar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi, rikicin Sudan ya zama mafi girman rikicin gudun hijira a duniya a tsakanin shekarar 2024 da 2025, lamarin da ya kara tabarbarewar al'amuran jin kai da kuma tunkarar bala'o'i mafi fi rikitarwa.

Rushewar Gininnukan More Rayuwa

Ambaliyar da aka yi a baya-bayan nan ta fallasa raunin ababen more rayuwa a Sudan, yayin da rikicin makami ya kai ga rufe kusan dukkanin ayyukan yau da kullum kamar kiwon lafiya, ilimi, ruwa, da wutar lantarki. Rikicin ya kuma yi tasiri ga rayuwar ‘yan kasar, wadanda ke fuskantar matsaloli masu yawa wajen samun takardun shaida kamar fasfo da katin shaida na kasa, a daidai lokacin da ake ci gaba da gurgunta ayyukan gwamnati da na hukumomi. Wadannan yanayi sun sanya duk wani bala'i ya zama barazana rubanye biyu da kuma shigar da kasar cikin tarin kalubale da ke bukatar daukar matakin gaggawa na kasa da kasa, ba wai kawai a magance illolin da ambaliyar ruwa ke haifarwa ba, har ma da samar da hanyoyin warware rikicin siyasa da na jin kai da ke barazana ga makomar Sudan.

Your Comment

You are replying to: .
captcha